BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari

'Yan bindiga na iya ta da Najeriya baki ɗaya - El-Rufai
Gwamnan ya ce ya sake jadaddawa shugaba Muhammadu Buhari matsayarsa na a ƙona dazuzzuka da waɗannan 'yan ta'adda ke ɓuya baki ɗaya.
KAI TSAYE An raba jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya na 2022
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
'Gwamnatin APC ba ta damu da rayuwar 'yan Najeriya ba'
PDP ta ce da gangan APC da gwamnatin Buhari suke bari ana kai hare-hare domin suna da alaka da 'yan ta'adda.
'Yan Majalisar wakilan Najeriya sun yi barazanar tafiya yajin aiki
Tabarbarewar tsaro a Najeriya ta sa 'yan majalisar wakilan kasar sun yi barazanar tafiya yajin aiki har sai sun ga canji.
Turai za ta bukaci China kada ta taimaka wa Rasha kan Ukraine
Tarayyar Turai za ta bukaci China da kada ta samar da makamai ga Rasha a yakin da take yi da Ukraine, sannan kuma kada ta taimaka wa Shugaba Putin a kan takunkumin da aka sanya masa.
Ku San Malamanku tare da Usman Isa Taliyawa Gombe
Sheikh Usman Taliyawa wanda ya shafe tsawon shekaru yana koyarwa da da'awa ya ce ba shi da wani buri a yanzu ganin ya rabu da duniya cikin imani da rufin asiri.
Bidiyo, 'Hanyoyin da muke bi wajen tantance ganin jinjirin watan Ramadan', Tsawon lokaci 3,38
Kwamitin duban wata na Najeriya ya umarci ƴan kasar da su fara duban jaririn watan azumin Ramadan daga ranar Juma'a.
Ku aiko mana salon girke-girkenku domin Ramadan
A wannan Ramadan ɗin BBC Hausa za ta zo maku da hanyoyin burge masu gida cikin sauki, tare da taimakon mata 'yan uwanmu ta hanyar koyon girke-girke.
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Mun gaza a matsayinmu na shugabanni a Najeriya - Nasir El-Rufai
Gwamnan wanda cikin yanayi mai cike da damuwa ya ce haƙiƙanin gaskiya yana cikin matuƙar baƙin ciki saboda rabonsa da ya yi bacci tun ranar Alhamis kuma baya iya bacci koda ya sha maganin bacci.
Ƴan bindiga sun fi gwamnatin Najeriya hanyoyin samun sahihan bayanan sirri - Bukarti
Barista Bukarti ya ce harin na nuna ƙarfin tattara bayanan da maharan ke yi, amma ita gwamnati ba ta iya tattara bayanai ta gane cewa suna shirya wannan ɓarnar ba.
‘Yan ci-ranin Afirka da kasar Italiya ke zargi da fataucin mutane
Daruruwan 'yan ci-rani, da yawa daga cikinsu kananan yara, suna kare rayuwarsu a kurkukun Italiya bayan an tuhume su da fataucin mutane.
Yawan kuɗaɗen da Rasha ke kashewa a yaƙin Ukraine
Ga takunkuman da ƙasashen yamma suka kakaba mata, Rasha na kashe maƙudan kuɗaɗe na soji don ɗaukar nauyin yakinta a Ukraine.
Ga wasu daga cikin waɗanda suka mutu a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna
Har yanzu ana cikin ɗimauta a Najeriya kan harin da aka kai wa jirgin ƙasa. Ga dai wasu daga cikin waɗanda aka samu tabbacin mutuwarsu.
'Yawan masu fama da talauci a Najeriya ya zarce miliyan 95'
Babban Bankin Duniya ya yi gargadin cewa yawan talakawan kasar zai fi miliyan 95 a bana.
Ruwa ya cinye mutane takwas yayin tsere wa harin ƴan bindiga a jihar Neja
Mutanen dai na ƙoƙarin tserewa daga ƙauyensu na Galkogo da ke yankin Munya ne sanadin wani hari da 'yan bindiga suka kai a ƙauyen.
Me ya ragewa ɗaliban Najeriya da rikici ya koro daga Ukraine?
Dubban daliban da suka tsere a yanzu sun shiga yanayi na tsaka-mai-wuya kan yadda za su ci gaba da karatu.
Yadda yankin Katari zuwa Rijana ya gagari jami'an tsaron Najeriya
Harin Litinin da daddare da 'yan bindiga suka kai tare da yin garkuwa da jama'a da dama a jirgin kasa da ke hanyar Kaduna daga Abuja ya sake jefa tsaro a zukatan matafiya.
Bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Usman Isa Taliyawa, Tsawon lokaci 11,56
Malamin wanda shi ne mataimakin Bala Lau shugaban kungiyar Izala a shirin Ku San Malamanku na BBC na wannan makon.
Bidiyo, Bidiyon yadda Osinbajo ya kai ziyara tashar jirgin ƙasa a Kaduna, Tsawon lokaci 1,31
Bidiyon yadda Osinbajo ya kai ziyara tashar jirgin ƙasa a Kaduna
Bidiyo, 'Ba zan manta da aikin da na yi lokacin mutuwar Abacha da Abiola ba', Tsawon lokaci 3,11
Tsoffafin ma'aikatan sun yi bayanai ne a kan yadda suka samu aikin BBC da yadda ya kasance musu, da rayuwa bayan sun bar aikin da dai wasu abubuwan da suka shafe su.
Bidiyo, Abin da majalisar dattawan Najeriya ta ce kan harin jirgin ƙasa a Kaduna, Tsawon lokaci 3,49
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci sojojin kasar su yi amfani da kayan fadan da gwamnati ta samar musu wajen yin luguden-wuta a kan maharan da ke addabar al`umma a shiyyar arewa maso yammacin kasar.
Bidiyo, Injiniya dan Najeriya da Turawa ke rububinsa, Tsawon lokaci 7,23
Malam Hadi Usman dattijo ne dan jihar Gombe da ke arewacin Najeriya wanda ya ƙera abubuwan fasaha da dama.
Bidiyo, Na samu matsala da iyayena lokacin da na kai masu Baturiya da nufin aure - Soja boy, Tsawon lokaci 4,18
Usman Umar wanda aka fi sani da soja boy ya ce ya sha gwagwarmaya da 'yan uwansa lokacin da ya kai masu baturiya Lisa gida da nufin aurenta.
Barcelona za ta kwashe 'yan Chelsea, Man Utd na sa ran tafiyar Ronaldo
Barcelona ta yi yunkurin cin moriyar takunkumin da aka sanya wa Chelsea, inda za ta dauke mata 'yan bayanta guda uku, yayin da Manchester United ke sa ran tafiyar Cristiano Ronaldo.
Abin da ya kamata ku sani kan jadawalin kofin duniya 2022
Ranar Juma'a za a raba jadawalin gasar cin kofin duniya da kasashe 32 za su kece raini a wasannin da za a yi a Qatar a Nuwamba zuwa Disambar 2022.
Augustine Eguavoen ya sauka daga muƙaminsa na kocin Najeriya
Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Augustine Eguavoen ya sauka daga muƙaminsa sakamakon kasa kai tawagar Super Eagles gasar Kofin Duniya ta Qatar 2022.
Man United za ta kara da Liverpool a Thailand a Yuli
Manchester United za ta fafata da Liverpool a wasan atisayen fuskantar kakar badi da za su kara a Thailand cikin watan Yuli.
Brazil ta koma mataki na daya a taka leda a duniya
Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta dare mataki na daya a jerin kasashen da ke kan gaba a taka leda a duniya a jadawalin da Fifa ta fitar ranar Alhamis.
Kante ya ƙi yarda ya koma PSG, Milan na son Assensio
Yada take kasancewa a kasuwar musayar ƴan wasan ƙwallon ƙafa ta Turai.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Ra’ayi Riga, 19:29, 1 Aprilu 2022, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 1 Aprilu 2022, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 1 Aprilu 2022, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 1 Aprilu 2022, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Bidiyo, ...Daga Bakin Mai Ita tare da Momee Gombe, Tsawon lokaci 6,12
A wannan kashi na 92, BBC ta tattauna da Momee Gombe, inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta.
Yadda wani sabon salon waka ya karbu a kasar Ghana
Salon wakar Asakaa na Ghana shi ne ke tashe yanzu a Afirka, bayan nasarar da salon wakar Afrobeats ya yi a duniya.
Shirye-shirye na Musamman
Saurari, Gane Mini Hanya: Yawan ƴan gudun hijira a Najeriya, Tsawon lokaci 12,14
Yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan bindiga da ke sanadin karuwar ƴan gudun hijira a arewa maso yammacin Najeriya, hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta kasar ta ce tana fadi-tashin inganta rayuwar dubban mabuƙatan da ake samu a kullum.
Saurari, Ko kin san hantara na hana yara tsawo?, Tsawon lokaci 15,11
Hantara da ke kai wa ga yawan damuwa a rayuwar yaro karami na hana shi ya yi tsawo kamar sauran sa'anninsa. In ji Likitoci.
Saurari, Ra'ayi Riga: Rikici kan gyaran dokar zaɓe, Tsawon lokaci 1,00,00
Ra'ayi Riga: Rikici kan gyaran dokar zaɓe
Saurari, Gane Mini Hanya: Hirar BBC da Sheikh Ibrahim EL-Zakzaky, Tsawon lokaci 13,56
Hirar BBC da Sheikh Ibrahim EL-Zakzaky – Kashi na farko
Kimiyya da Fasaha
Bidiyo, Ƴan sama jannatin Rasha da Amurka sun ce lafiya lau suke zaune a sararin samaniya, Tsawon lokaci 0,54
An dai rika fargabar cewa Rasha za ta ƙi ɗauko Ba'amurken daga tashar sararin samaniyar -- sai dai da wuya Amurka ta sake neman taimakon Rasha wajen jigilar 'yan sama jannatinta.
Yadda yaƙin Rasha ke barazana ga hadin kan binciken sararin samaniya
Yaƙin Ukraine na barazanar kawo karshen haɗin-kai tsawon shekaru tsakanin Rasha da kasashen yamma kan shirin binciken sararrin samaniya.
Hotuna
Hotunan majami'u da wuraren tarihi na addini da aka ɗaiɗaita saboda yakin Ukraine
Hotunan majami'u da wuraren tarihi na addinin Ukraine da hare-haren dakarun Rasha suka lalata.
Mutum-mutumi da mai daukar kara na cikin hotuna Afirka na wannan makon
Ga kayatattun hotunan na wannan makon daga sassan Afirka da ma wasu wuraren.
Labaran TV
Labaran Talabijin
Ku kalli labaran talabijin a duk lokacin da ku ke bukata wanda muke gabatarwa daga ranar Litinin zuwa Juma'a da karfe takwas na dare a agogon GMT.
Labarai Cikin Sauti
Saurari, Minti Daya Da BBC Na Rana 01/04/2022, Tsawon lokaci 0,52
Minti Daya Da BBC Na Rana 01/04/2022
Korona: Ina Mafita?
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku na tsawo minti hudu domin wayar da kan jama’a kan cutar Coronavirus da ta addabi kasasshen duniya.
Yadda ake amfani da harshe a aikin jarida
Ƙila à iya cewa mafi muhimmanci a aikin jarida shi ne harshe. Yin amfani da harshen da ya dace ba tare da kuskure ba yana ba ‘yan jarida damar samar da rahotanni da labarai ba tare da kuskure ba.
Dabarun Yin Rahoto Mai Kyau
Dabarun Yin Rahoto Mai Kyau
Aikin jarida na hazaƙa
Aikin jarida aiki ne na ƙwaƙwalowa da gabatar wa jama’a sabon labari koyaushe. Yana buƙatar iya tallatawa a gaban edita. “Lalle ka zama mai ƙwaƙwar sanin komi yadda har ba za ka iya kallon bangon da babu komi kansa ba ba tare da ka yi mamakin me ya sa ba a rubuta komi a kansa ba.”
Ko ya kamata a ce Mista Buhari a labarun Hausa?
Ko ya kamata a ce Mista Buhari a labarun Hausa?
Domin ma'abota BBC
Africa TV
Original and high-impact BBC investigations from across Africa
A BBC Africa daily round-up of business news, with insight from African entrepreneurs
Pan African BBC discussion TV programme, exploring the life experiences of women in today’s Africa.
Weekly BBC Africa programme on health, food and lifestyle trends